26 Satumba 2026 - 23:44
Source: ABNA24
Lavrov: Hari Kan Cibiyoyin Nukiliya Na Iran, Barna Ce Da Ba Za A Iya Gyara Ta Ba Bisa Kimar Hukumar Makamashin Nakilya Ta Ƙasa Da Ƙasa

Sergei Lavrov, ministan harkokin waje na Rasha, a cikin jawabinsa a Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya, ya kwatanta harin da Amurka da gwamnatin Sahayoniya suka kai kan cibiyoyin nukiliya na Iran a matsayin rauni da ba za a iya gyara ba ga suna da ikon Hukumar Makamashin Atom ta Ƙasa da Ƙasa kuma ya nemi a amince da gwamnatin Falasɗinu a hukumance da kuma sakin Nicholas Maduro da matarsa nan take.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Sergei Lavrov, ministan harkokin waje na Rasha, a cikin jawabinsa a Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya tare da sukar hare-haren Amurka da gwamnatin Sahayoniya kan cibiyoyin nukiliya na Iran, ya ce waɗannan hare-haren sun yi barnar da ba za a iya gyara ta ba ga kima da ikon Hukumar Makamashin Nukliya ta Ƙasa da Ƙasa.

Lavrov a cikin jawabinsa ya ce: kai hari kan cibiyoyin nukiliya na Iran waɗanda a cewarsa suna ƙarƙashin sa ido da garantin Hukumar Makamashin ta Ƙasa da Ƙasa, ya yi mummunan tabo da ba za a iya gyara ba ga kumar wannan cibiyar.

Ministan harkokin waje na Rasha, ya zargi Amurka da Isra'ila da kai hari kan ababen more rayuwa na fararen hula da cibiyoyin nukiliya na Iran kuma ya kira waɗannan matakan "mamaya."

Lavrov ya kuma yi nuni da ci gaba da rikice-rikicen makamai a yankin tekun Farisa da kewayen mashigar Hormuz ya ce: ci gaba da wannan yanayi yana lalata zirga da jigilar sufurin ruwa da kasuwancin duniya.

Ya nanata warware rikicin da ke akwai yana buƙatar samar da amincewa tsakanin Iran, ƙasashen gefen tekun farisa da sauran ƙasashen Larabawa.

Ministan harkokin waje na Rasha ya ƙara da cewa: Moscow a shirye take tare da sauran ƙasashe, ta shiga cikin ingantaccen tsari don taimakawa wajen samar da kwanciyar hankali a yankin yammacin Asiya; yankin da a cewarsa yana da muhimmanci na dabarun.

Lavrov a wani ɓangare na jawabinsa, ya ɗauki amfani da ƙarfi wajin kashe jagoran Iran, iyalinsa da jami'an wannan ƙasar a matsayin abin da ba za a Aminta da shi ba kuma ya ce Rasha tana ƙin irin waɗannan matakan.

Ministan harkokin waje na Rasha ya kuma yi nuni da abubuwan da ke faruwa a Venezuela kuma ya nanata sakin Nicholas Maduro, shugaban Venezuela da aka sace, da matarsa nan take.

Lavrov ya ce: Moscow tana neman irin waɗannan abubuwan kada su sake faruwa a nan gaba kuma a daina amfani da matakan tilastawa kan gwamnatoci masu zaman kansu.

Ma'aikatar harkokin waje ta Rasha ma a ganawar ranar 26 ga Satumba da Lavrov ya yi da Ivan Gil, ministan harkokin waje na Venezuela, ta nanata adawar Moscow ga amfani da matakan tilastawa kan gwamnatoci masu zaman kansu.

Lavrov a ci gaba da jawabinsa ya ce: Rasha tana ganin lokaci ya yi da za a amince da gwamnatin Falasɗinu.

Ya na mai cewa: ba tare da kafa da amincewa da gwamnatin Falasɗinu ba, samun aminci mai ɗorewa a Gabas ta Tsakiya ba zai yiwu ba.

Maganganun Lavrov sun zo ne a yanayin da yaƙi da rikice-rikice da dama a yammacin Asiya suka kasance daga cikin manyan batutuwan tattaunawar Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya a wannan shekara.

……………

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha